Asad;Nasarorin Da Syria Ta Samu Sakamakon Goyan Bayan Iran Ne.

  • Lambar Labari†: 802713
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Shugaban na Kasar Syria ya kara da cewa ba domin goyin bayan Iran ba, to da Syria ba ta samu nasarar da ta samu ba.

Kamfanin dillancin labarun "Iran" ya bada labarin cewa; Shugaba Bashshar Asada ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugaban kwamitin tsaron kasa da siyasar waje, a majalisar shawarar musulunci ta Iran, Ala'uddin Brujardi.

A nashi gefen Burujardi ya taya gwamnati da al'ummar Syria murnar 'yanto da birnin Halab, daga hannun 'yan ta'adda. Ya kuma kara da cewa kwato Halab, din ya yi daidai da yanayin da Iran ta kwato da birnin Khurramshahr a cikin watan Mayu na shekarar 1982.

Iran da Syria da Rasha suna da cibiyar tuntubar juna dangane da abinda ya ke faruwa a cikin kasar ta Syria.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky