An Kama Mutane 16 Da Ake Zarginsu Da Hannu A Kai Harin Turkiyya

  • Lambar Labari†: 802493
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Rahotanni daga Turkiyya na cewa mutane 16 ne kawo yanzu aka cafke bisa zarginsu da hannu a harin da wani dan bindiga ya kai a gidan rawan na Reina dake birnin Istambul.

Daga dai cikin wadanda ake tsare da har da wasu 'yan kasashen waje biyu da aka cafke a daidai lokacin da suke shirin barin kasar a filin sauka da tashin jiragen sama na Ataturk dake birnin na Istambul kamar yadda kanfanin dilancin labaran kasar na Dogan ya rawaito.

Saidai har kawo yanzu ba'a bayyana asalin 'yan kasashen wajen da aka cafke.

kungiyar 'yan ta'addan IS ce dai ta dauki alhakin kai harin, a yayin da 'yan Sanda Turkiyya ke ci gaba da farautar mutimin da ya bude wuta a gidan rawan inda ya kashe mutum 39 ciki har da 'yan kasashen waje da dama bayan raunana wani adadi mai yawa.

Da sanyin safiyar ranar 1 ga wata ne, dan bingida ya kutsa kai cikin gidan rawa, inda ya yi harbin kan mai uwa da wabi, kan wadanda ke bikin sabuwar shekara.

Daga bisani dai dan bindigar ya tsere, amma a halin yanzu 'yan sanda sun dukufa domin farautarsa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky