Iran Ta Karyata Cewa Saudiyyah Ta Bukaci Su Zauna Kan Batun Hajji Mai Zuwa

  • Lambar Labari†: 802295
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Shugaban hukumar alhazai ta kasar Iran Hamid Muhammadi ya karyata batun cewa Saudiyyah ta aike da wasika ga ma'aikatarsa domin gayyatarsu zuwa tattaunawa kan aikin hajji mai zuwa.

A zantawar da ya yi jiya da manema labarai a hukumar radiyo da talabijin ta kasar Iran a birnin Tehran, shugaban hukumar alhazan ta kasar Iran ya bayyana cewa, ba su samu wata wasika daga bangaren Saudiyyah ba, amma idan har gwamnatin ta Saudiyyah da gaske take Iran ba ta da wata matsala kan hakan, amma hakan dole ne ya biyo bayan bude ofishin jakadancin Iran da ke Riyad da kuma sauran kananan ofisoshinta da ke Makka da Madina da kuma Jidda, wadanda masarautar ta Saudiyyah ta rufe.

A ranar Alhamis da ta gabata ce dai ministan ma'aikatar kula da harkokin aikin hajji a Saudiyya Muhammad Bin Tan ya bayyana cewa, sun aike wa hukumar alhazai ta kasar Iran da wasika, domin a zauna a tattauna batun batun halartar alhazan Iran a aikin hajji mai zuwa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky