Miliyoyin Al'ummar Iran Sun Gudanar Da Jerin Gwanon Tunawa Da Ranar 9 Ga Watan Dey

  • Lambar Labari†: 801512
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Miliyoyin al'ummar Iran ne suka fito kan titunan garuruwa da biranen kasar don gudanar da jerin gwanon tunawa da ranar 9 ga watan Dey, wato 30 ga watan Disamban 2009 ranar da al'ummar kasar suka fito don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci na kasar a lokacin da makiya suka yi na haifar da fitina bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2009.

Rahotanni daga bangarori daban-daban na Iran din suna nuni da cewa tun da safiyar yau ne al'ummar garuruwa da birane daban-daban na Iran din ciki kuwa har da birnin Tehran babban birnin kasar ta Iran don gudanar da jerin gwanon da kuma sake jaddada goyon bayansu ga tsarin Musulunci da ke iko a kasar.

Rahotannin dai sun bayyana cewar masu jerin gwanon suna dauke ne da kwalaye da kyallaye bugu da kari kan hotunan marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma na Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei don sake nuna goyon bayan ga juyin juya halin Musulunci da kuma koyarwar marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma sake jaddada mubaya'arsu ga Jagora Ayatullah Khamenei, bugu da kari kan yin Allah wadai da gwamnatin Amurka da sauran makiya wadanda suke adawa da kuma kokarin ganin bayan tsarin Musuluncin.

A ranar 30 ga watan Disamban 2009 ne dai miliyoyin al'ummar Iran din suka fito kan tituna kasar wajen yin Allah wadai da wadanda suka tayar da fitinar da ta faru a wasu garuruwa na kasar bayan da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a shekara ta 2009 din. To tun daga wancan lokacin a duk lokacin da shekara ta zagayowa akan gudanar da irin wadannan tarurruka don nuna goyon baya  ga tsarin Musuluncin.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky