Sheikh Na'im Kasim: Batun Palastinu Shi Ne Tushen Hadin Kan Musulmi A Yanzu

  • Lambar Labari†: 798631
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na'im Kasim ya bayyana batun 'yantar da Palastine daga mamayar yahudawa a matsayin babban tushen hadin kan al'ummar musulmi a wannan zamani.

Sheikh Na'im Kasim ya bayyana hakan ne a gaban taron makon hadin kai da aka fara gudanarwa a jiya a birnin Tehran, wanda yake samun halartar manyan malamai da masana daga kasashen duniya daban-daban, inda ya ce a halin yanzu babban ma'auni na gane gaskiya mai kira zuwa hadin kan al'ummar musulmi shi ne matsayarsa dangane da batun Palastinu da kuma mamayar da yahudawan sahyuniya suke yi wa masallacin Quds.

Ya ce duk wanda yake ikirarin musulunci a duniyar yau, amma bai damu da halin da al'ummar musulmi na Palstinu suke ciki ba da kuma masallacin Quds, to maganarsa  a fatar baki ce kawai.

Dangane da halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da ke fama da matsalar 'yan ta'adda kuwa, Sheikh Na'im ya bayyana cewa, babbar manufar haifar da ta'addanci a cikin kasashen larabawa da na msuulmi musamman a  kasashen yankin gabas ta tsakiya, shi ne janye hankulan al'ummomin duniya daga barnar da Isra'ila take tafkawa a kan musulmin  Palastinu, da kuma wasu rusa kasashen da Isra'ila take kallonsu a matsayin barazana a gare ta, abin da yake faruwa a Syria da Iraki ya isa ya zama babban misali kan hakan.

A bangare guda kuma, ya kirayi al'ummar musulmi da su zama cikin fadaka, musamman ma yadda a halin yanzu makiya muslunci suke amfani da wasu daga cikin manyan kasashen larabawa wajen aiwatar da bakaken manufofinsu a kan musulmi da rusa su, ba tare da sun ankara ba, kuma abin bakin ciki shi ne, ana aiwatar da manufofin makiya muslunci a kan musulmi ne da sunan yada addini, kamar yadda irin wadannan kasashe suke yada ta'addanci domin kare manufar Isra'ila da Amurka da turawan yamma ta hanyar karfafa 'yan ta'adda da fatawowin kafirta musulmi da yin kisan gilla a kan mata da kanan yara da sunan suna taimaka ma masu jihadi a tafarkin sunnar manzo, wanda hakan yake kara bata sunan muslunci da sunnar manzon Allah a idon duniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky