Maulidin Manzon Allah {s.w.a.a} A Kasar Burtaniya

  • Lambar Labari†: 797864
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Musulmin kasar Birtaniya sun gudanar da jerin gwanon murnar maulidin manzon Allah (SAW) a birane daban-daban na kasar, da hakan ya hada da birnin London da Tottenham da ma wasu biranan.

Shafin yada labarai na jaridar Tottenham Post ya bayar da rahoton cewa, a yau daruruwan musulmi mazauna birnin sun gudanar da jerin gwano cikin lumana, domin nuna murnarsu da zagayowar maulidin manzon Allah (SAW).

Rahoton ya ce musulmin sun rika daga kyallaye masu launin kore da fari, domin nuna sakon zaman lafiya irin na addinin muslunci ga sauran dukkanin al'ummomi.

Nadim Amin daya ne daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wadannan taruka a kasar Birtaniya, ya bayyana cewa suna shirya tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a kowace shekara, a wannan shekara suna yin amfani da wannan damar domin kara wayar da kan jama'a wadanda ba musulmi kan sakon aminci da kaunar juna tsakanin 'yan adam da manzon Allah ya zo da shi.

Ana gudanar da irin wadannan taruka dai a kasashen musulmi da dama, wanda akasari an fara su ne daga yau, yayin da kuma wasu sun fara gudanar da tarukan nasu tun daga lokacin da wannan wata mai albarka ya tsaya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky