Rauhani: Hadin Kai Shi ne Tushen Karfin Al'ummar Musulmi

  • Lambar Labari†: 797617
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Shugaban Kasar Iran: Tushen Karfin Musulmi Shi ne Hadin Kai.

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya ce;  Tarihin Manzon Allah (s.a.w.a) shi ne abin koyi ga musulmi.

shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran, Dr. Hassan Rauhani wanda ya gana da musulmi mabiya mazhabobin sunna anan Iran a ranakun maulundin manzon Allah (s.a.w.a) ya kara da cewa; Kabilu da kuma mazhabobi mabanbanta da ake da su, wara babbar dama ce ta hada kan kasa da kuma ci gaban al'umma, bai kamata a dube su a matsayin barazana ba.

Da ya ke magana akan kungiyoyi masu kafirta musulmi, Dr. Hassan Rauhani ya ce; Ba su da wani aiki da ya wuce bakanta sunan musulunci da musulmi a duniya.

A Iran ana raya bukukuwan Mauludi ne daga ranar 12 ga watan Rabi'ul Auwal zuwa 17 gare shi, bisa banancin riwayoyin haihuwar fiyayyen halitta a tsakanin sunnan da shi'a.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky