A saki jagoran mu Sheikh El-Zakzaky - Takardar manema labarai da aka raba

  • Lambar Labari†: 738654
  • Taska : Harkar musulunci a Nigeria
Brief

A kwana a tashi har mun doshi kwanaki casa’in cikin jimamin mummunan harin da rundunar sojin gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kai wa ’yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a birnin Zazzau. Zai yi kyau a wannan rana ta jimami, mu yi tilawa a takaice na irin ta’addancin da aka yi wa ’yan uwa musulmi bisa.

A SAKI JAGORANMU SHAIKH ZAKZAKY
 

A kwana a tashi har mun doshi kwanaki casa’in cikin jimamin mummunan harin da rundunar sojin gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kai wa ’yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a birnin Zazzau. Zai yi kyau a wannan rana ta jimami, mu yi tilawa a takaice na irin ta’addancin da aka yi wa ’yan uwa musulmi bisa umurnin zababbun shugabannin Kasar nan.

An kashe mata da yara kanana. Wani da ya je mucuwaren Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya ya fadi cewa ya ga gawawwakin ’yan uwa mata tamanin, kafin sojoji su zo su kwashe su. Cikin yara kanana kuwa da ake da tabbacin kashe su da sojoji suka yi har da Batula Buhari Jega, yarinya ’yar shekara daya da rabi kacal.

An kashe daliban Jami’o’i, Kwalejojin kimiyya da fasaha, Kwalejojin ilimi da makarantun sakandaren da har yanzu ba a kai ga kididdige su ba. Amma Dandalin dalibai na Harkar Musulunci (Academic Forum) ya fadi a gangamin da ya yi a Abuja kwanan nan cewa, suna da kididdigar bacewar dalibai 30 da suke Jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare.

An kashe ’yan uwa musulmi sama da dubu guda. Tabbaci hakika akwai sunayen mutane 750 da kawo yanzu ake da su, wadanda ba a gan su ba tun bayan ranar Asabar 12 ga Disamba, 2015.

An sake kashe ’ya’yan Jagoranmu Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky guda uku a gabansa. Sune: Hammad, Aliy da Humaid. Da ma kuma a 2014 sojojin sun kashe Ahmad, Hamid da Mahmud.

Kawo yanzu babu gawa ko daya da gwamnatin Tarayya ta ba iyalai da dangin wadanda sojoji suka kashe. Bilhasali ma Janar Buratai cewa ya yi wai mutum bakwai kawai suka kashe.

An harbi Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky har sau shida. An kuma harbi matarsa, Malama Zeenah Ibrahim sau biyu a jikinta.

An raunata ’yan uwa musulmi maza da mata bila adadin. Wadanda Allah ya yi da sauran kwanansu, kuma yanzu haka ko dai sun gama jinya, ko kuma suna cikin ta.

An azabtar da ’yan uwa musulmi maza da mata da nau’o’in azabtarwa kala-kala. Mafi muni shi ne kware wa ’yan uwa mata hijabi da sojoji suka yi, da ma zargin yin fyade ga wasu ’yan uwa mata da suka kashe daga bisani.

An rusa cibiyar Musulunci ta Husainiyya da ke titin Sokoto road, da kuma Cibiyar yin fim da makabartar shahidai da ke Darur Rahma a hanyar Jos, da Fudiyya Islamic Centre da ke Dan Magaji, da gidan da a ciki akwai kabarin Mahaifiyar Shaikh Zakzaky da ke Jushi. An yi rusau din nan ne tare da barin barayin gari su sace duk wani abu mai amfani a wadannan wurare. Wasu marasa imanin ma har kudade da zobuna da wayoyin mamatan da ke wuraren suka sace.

Ya jama’a wannan fa a takaicen takaitawa ne muka kawo su. A halin yanzu kuma sai ga shi ana zama a Hukumar binciken wannan tua’annati da sojoji suka yi, alhali an danne wa Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky damar da tsarin mulki da duk wata doka ta shari’a a kasar nan suka ba shi na ya gana da Lauyoyinsa. Lauyoyin nan sun jejje inda ake tsare da Shehin Malamin har sau hudu, amma ana dakile bukatarsu na su gana da shi. In wannan ba take-taken ci gaba da yi mana rashin adalci ba ne, mene ne?

Abin da duk wannan ta’annuti da sojoji suka yi a Zariya ke nunawa shi ne Musulunci da musulmi aka yi nufin murkushewa. Kuma in jama’a ba su dunkule wajen Allah wadai da neman a yi adalci a kan wannan batu ba, to fa in yau an yi wa ’yan uwa musulmi na Harkar Musulunci, to gobe kuma wata jama’ar ta musulmi za a auka wa. Tun ba a yi nisa ba har mun soma jin Malaman da suka goyi bayan kisan gillan da aka yi mana, wanda gwamnatin Elrufa’i take da hannu dumu-dumu a ciki, sun soma cewa gwamnatin Elrufa’i tana fa]a ne da Musulunci shi ya sa take neman kafa dokar wa’azi a jihar. Don haka ba za mu gushe ba muna yin addu’o’i na kai kukanmu ga Allah Ta’ala a kan cewa duk wanda yake da hannu a wannan mummunan take hakkin bil’adama, kada Allah ya ba shi abin da yake so duniya da lahira.
Muna kuma kara jaddada bukatunmu kamar haka: A saki jagoranmu Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky da iyalinsa da ke tsare ba tare da wani sharadi ba. A saki dukkan ’yan uwa musulmi da muka san ake tsare da su da wa]anda ba mu san ma ana tsare da su ba. A biya mu diyyar rayuka da dukiya da aka salwantar a yayin wannan hari na kwanaki uku a Zariya.

Sa hannu

Malam Abdulhamid Bello
03-03-16


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

asura-mystery-of-creation
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky