Kungiyar Kiristoci [CAN] reshen Katsina ta yi jaje akan harin Sojoji a Zariya

  • Lambar Labari†: 725153
  • Taska : Harkar musulunci a Nigeria
Brief

Wata tawaga ta 'ya'yan kungiyar mabiya addinin kirista watau CAN reshen jihar Katsina ta yi jaje akan irin ta'addancin sojojin gwamnatin Nigeria akan Harkar Musulunci da kuma yin kutse a gidan jagoran Harkar a gidan sa dake unguwar Gyallesu Zariya, wanda ya yi sanadin shhadar 'yan uwa da yawa tare da jikkita wasu masu yawa

A jiya Talata ne tawagar ta kawo ziyara ta musamman ga wakilin 'yan uwa na garin na Katsina Malam Yakubu Yahaya inda suka mika masa takarda ta ta'aziyyar su tare da yin jaje.

Kungiyar ta CAN ta bayyana rashin jin dadin ta kan abin da ya faru sannan kuma tayi fatan wannan abu ya kawo karshe.

Malam Yakubu Yahaya ya karbe su hannu biyu-biyu sannan yayi godiya kan wannan nuna damuwar da suka yi.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky