Sojoji sun ci gaba da kai hare-hare har zuwa Gyallesu, unguwar Sheikh Zakzaky

  • Lambar Labari†: 724523
  • Taska : Harkar musulunci a Nageria
Brief

Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan hare-haren da sojoji suka kai a Husainiyar Baqiyyatullah, yanzun haka kuma sun nufi unguwar Gyallesu inda jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky ke da zama kuma an ji karar harbe-harbe a can.

Rahotannin sun ci gaba da bayana cewa sojoji suna harbi ne kawai ga duk wanda suka ci karo da shi wanda yayi musu kama da musulmi.

Haka nan kuma rahotannin sun ci gaba da bayyana cewa ana ta ci gaba da karo sojoji zuwa wannan rukunin na unguwar Gyallesu.

Rahotanni sun tabbatar mana da cewa kawo ya zuwa yanzun an sami akalla shahidai 5 sannan kuma wasu kimanin 40 sun ji raunuka a hare-haren Gyallesu.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky