Tutar ya Hussain{A.S} a Kofar Fadar White House

  • Lambar Labari†: 723555
  • Taska : ABNA
Brief

Daruruwan ‘yan shi’a mazauna Amruka ne suka gabatar da juyayin Arba’in na Imam Hussain{a.s} a bakin fadar white House, kuma sukayi Allah wadai da ‘yan ta’adda da ta’addanci

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-daruruwan mabiya Ahlul-baiti ne a jiya lahadi suka gabatar da taron juyayin Arba’in na Imam Hussain{a.s} a washington babban birnin kasar Amruka a lokaci guda kuma sukai Allah wadai da yan ta’adda.

Taron dai an gudanar da shi a kofar fadar white House inda mahalarta taron suka sa bakaken kaya dauke da tutar ya Hussain kuma mafiya yawansu sun fitone daga birnin na Washington wadan da suka hada maza da mata da kuma kananan yara dauke da kwalaye na la’antar yan kungiyar ta’adda ta da’ish.

Mahalarta taron sun raba biredi ga masu wucewa da yan kallo.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky