Zanga-zangar kyamar musulunci a Australia

  • Lambar Labari†: 701577
  • Taska : RFI
Brief

An yi arangama tsakanin kungiyoyi ma su kyamar addini Islama da wandada ke adawa da wariyar launin fata a kasar Australia, lamarin da ya haifar da rudani da har ya tilastawa ‘yan sanda soma yin kame domin hana yaduwar rikici.

Zanga zangar ta lumana da aka soma a birnin Melbourne ta ya biyo bayan adawa ne da wasu masu kyamar addinin islma suka shirya dangane da da yadda wata kafar yadda labarai ke bawa yan kungiyoyin ta’ada mahinmancin a shirye shiryenta abinda suke ganin babban barazana ce ga al’ummar kasar .

Akwai kuma yan kungiyar da ke adawa da matakin kasar ta Australia na kyamar yan cirani a kasar

Sai dai arangama tsakanin kungiyoyin ya soma daukar sabon salo abinda yasa Yansanda ala tilas suka yi anfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa su

Wani kwamishanan yan sanda a kasar da ya kare matakin yansanda na yin anfani da barkonon tsohuwa ya ce basu da matsala idan har za’a gudanar da zanga zanga cikin lumana sai dai zasu dauki matakai irin hakan domin hana barkewar rikici a kasar.

Kazancewar gangami dai ya samo asali ne bayan al’ummar kasar na kare matakin kasar ta Australia na goyon bayan ta na yakin da masu tsautsauran ra’ayi islama da ayyukan su dake ta tayar da hankulan al’ummar dunioya yayin da wasu yan tsiraru yan kasashen waje dake zaune a kasar ke adawa da yadda gwamnatin ke kin karbar bakin haure dake kokarin samun mafaka a kasar

Yanzu haka dai an tsare mutane uku da ake zargi da laifin tayar da rikici a cikin kasar288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky