Yan sanda a Birnin New york sun gudanar da zanga-zanga

  • Lambar Labari†: 662764
  • Taska : ABNA
Brief

A jiya ne mutane Birnin New york na Amurka suka tashi da abun mamaki ganin jama'in yan sanda na gudanar da zanga-zanga sabanin yanda a ka saba ganin masu kiyyaya da wariyar launin fata na gudanarwa.

Kamfanin Dillanci labarai na Ahlulbati{a.s}-Abna- a satukan dauka wuce garin New york ya hadu da zanga-zangar nuna rashin amincewa da nuna bam-bamcin launin fada da yan sandar kasar Amurka ke nuna ma bakaken fata.

Amma wannan satin zancen ya canza launi domin kuwa a jiya jami'an yan sanda ne suka gabatar da zanga-zangar. Dubannin yan sanda ne suka shiga cikin sahun zanga-zangar bayan sun gudanar da zana'idar daya daga cikin abokanin aikin su.

Masu jerin gwanon sun nuna rashin jin dadin su a kan maganar da kwamnan garin Birnin yayi, inda yake cema dansa da yayi hattara da yan sanda.

A cewar su irin wannan zancen ya  kara kawo kiyyaya ga yan sanda kuma yasa mutane basu ganin su da daraja wanda hakan yai sanadiyar kashe yan sanda biyu a satukan da suka gabata.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky