Ganawar malaman Ahlulsunna na kasar portigal da shugaban cibiyar Ahlulbait{a.s} ta duniya.

  • Lambar Labari†: 661206
  • Taska : ABNA
Brief

Shugaban cibiyar Ahulbait{a.s}ta duniya ayayi ziyararsa kasar portigal ya gana da wani sashe na malaman Ahlulsunna na kasar.

Tashar labarai ta Ahlulbait{a.s}-abna- ta rawaito shugaban cibiyar  ta Ahlulbait{a.s} wanda ke ziyarar aiki a kasar portigal ya gana da wani sashe na maluman Ahlulsunna na kasar a cibiya musulunci dake lesbon babban birnin kasar.

Hujjatulislam muhammad muhsin akhtari, a yayin ganawar yayi ishara da halin da yan ta'adda suka saka duniyar musulmi aciki ya kara da cewa yan gunkiyar takfiri ta da'ish wadanda suka sa ta'addanci a gaba, suna bata fuskar musulunci a duniya don haka ya zama dole maluman addini su tashe tsaye domin bayyana addini na gaskiya ga fuskar duniya.

Ya cigaba da cewa; ta'addancin da da'ish ke aikatawa zai sa tambaya akwakwalen wadanda ba musulmi ba cewa shin haka addini musulunci yake? Don haka wajibi ne mu sanarda wadanda ba musulmi ba hakikanin musulunci.

A wani bangare na bayaninsa yayi kira ga hadin kan musulmi shi'a da sunna, bam-bamcin dake tsakani shi'a da sunna ya samu ne sakamakon hura wutar da makiya keyi, saboda tun farko mabiyan  wadannan mazahabobin suna da hadin kai da girmama junan su. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky