Iran, ta sanar a wannan Talata da kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta tsakaninta da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, kamar yadda majalisar dokokin kasar ta bukata, idan dai har Amurka ba ta dage wa kasar takunkumi ba zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.
cigaba ...-
-
Gwamnatin Iran Ta Yi Maraba Da Umurnin Imam Khamenei Na Daga Murya Gaba Daya Na Bukatar A Dagewa kasar Takunkuman Tattalin Arziki
Faburairu 24, 2021 - 1:53 PMGwamnatin kasar Iran ta bayyana anniyarta na ganin an daga murya guda a duk fadin kasar don ganin an kawo karshen takunkuman zalunci da Amurka ta dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayanin da gwamnatin kasar ta fitar a yau wanda yake maraba da umurnin Imam Aliyul Khaminae na yin haka.
cigaba ... -
Daga Gobe Talata, Iran Ba Za Ta Sake Barin Masu Sa-Ido Su Ziyarci Cibiyoyinta Na Nukiliya Ba
Faburairu 23, 2021 - 2:57 PMShugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, ya bayyana cewa; aiki da tsarin sanya idon na ba zata, zai tsaya baki daya daga gobe Talata 23 ga watan nan na Febrairu.
cigaba ... -
Allah Ya Yi Wa Fitaccen Dan Gwagwarmaya Anis Naqqash Rasuwa
Faburairu 23, 2021 - 2:52 PMA yau ne Allah ya yi wa fitaccen dan gwagwarmaya da mamayar Isra’ila a kasashen musulmi da na larabawa Anis Naqqash rasuwa.
cigaba ... -
Imam Khamenei: Iran Za Ta Iya Kara Yawan Uranium Da Take Tacewa Daga Kashi 20% Har zuwa 60%
Faburairu 23, 2021 - 2:48 PMJagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran ya bayyana cewa, Iran za ta iya tace sanadarin uranium daga kashi 20% zuwa kashi 60% matukar dai tana da bukatar yin hakan.
cigaba ... -
Musulmin Uyghur Na Kokawa Kan Matakan Da Gwamnatin China Take Dauka Domin Takura Su
Faburairu 23, 2021 - 2:46 PMShugaban gayammar kungiyoyin musulmin kabilar Uyghur Isa Dulkun, wanda kuma dan siyasa ne mai wakiltar yankinsa a kasar China, ya bayyana cewa, ko shakka babu a cikin shekarun baya-bayan nan gwamnatin kasar tana daukar matakai na takura wa musulmin Uyghur na kasar da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi, wanda hakan ba gaskiya ba ne.
cigaba ... -
Gwamnatin Iran Ta Yi Maraba Da Umurnin Imam Khamina’e Na Daga Murya Gaba Daya Na Bukatar A Dagewa kasar Takukuman Tattalin Arziki
Faburairu 23, 2021 - 2:42 PMGwamnatin kasar Iran ta bayyana anniyarta na ganin an daga murya guda a duk fadin kasar don ganin an kawo karshen takunkuman zalunci da Amurka ta dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayanin da gwamnatin kasar ta fitar a yau wanda yake maraba da umurnin Imam Aliyul Khaminae na yin haka.
cigaba ... -
Iran Za Ta Rage Aiki Da Bai Wa Masu Sa-Ido Damar Ziyartar Cibiyoyinta Na Nukiliya A Duk Lokacin Da Su Ka Ga Dama
Faburairu 21, 2021 - 2:09 PMMataimakin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Iraqchi ya sanar da cewa, matakin yana nufin fage bai wa masu sa ido din damar kawo ziyara ta ba-zata a duk lokacin da su ka ga dama da kaso 20 zuwa 30%.
cigaba ... -
Shugaban Kasar Iran Hassan Rauhani Ya Kira Yi Amurka Da Ta Koma Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliya
Faburairu 19, 2021 - 10:02 PMShugaban na Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya kira gwamnatin Amurka da ta yi aiki da nauyin da ya rataywa a wuyanta dangane da yarjejeniyar Nukiliya, kuma ta yi aiki da kudurin MDD, mai lamba 2231.
cigaba ... -
Imam Khamenei: Juyin Juya Halin Muslunci Ya Wanzu Ne Sakamakon Imani, Juriya, Da Sadaukarwa
Faburairu 18, 2021 - 10:48 AMJagoran juyin juya halin muslunci a Iran Imam Khamenei ya bayyana cewa, juyin juya halin muslunci a Iran ya wanzu ne sakamakon juriya, sadaukarwa da kuma imani da Allah madaukakin sarki.
cigaba ... -
Nasrullah: Isra’ila Za Ta Fuskanci Martani Mafi Tsanani Idan Da Bude Wani Sabon Yaki A Kan Lebanon
Faburairu 18, 2021 - 10:31 AMBabban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, Isra’ila za ta fuskanci martani mafi muni a tarihinta, matukar dai ta yi gigin sake shiga wani sabon yaki da kasar Lebanon.
cigaba ... -
Iran Da Qatar Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin
Faburairu 16, 2021 - 3:23 PMMinistan harkokin wajen kasar Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, ya fara wata ziyarar aiki a nan birnin Tehran.
cigaba ... -
Sojojin Kasa Na Iran Sun Gwada Sabon Makami Mai Linzami Mai Sarrafa Kansa Da Ke Cin Zangon Kilo Mita 300
Faburairu 15, 2021 - 3:59 PMSojojin Kasa Na Iran Sun Gwada Sabon Makami Mai Linzami Mai Sarrafa Kansa Da Ke Cin Zangon Kilo Mita 300
cigaba ... -
Iran Tana Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Yemen Ta Hanyoyi Na Diflomasiyya
Faburairu 14, 2021 - 5:32 PMJakadan kasar Iran a birnin San’a na kasar Yemen ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan ganin an warware dukkanin matsalolin kasar Yemen ta hanyoyi na siyasa.
cigaba ... -
Araqchi: Yarjejeniyar Nukiliya Ba Ta Da Amfani Ga Iran Matukar Ba A Dauke Mata Takunkumi Ba
Faburairu 13, 2021 - 3:30 PMMataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa, yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ba ta da wani amfani ga kasar ta Iran, matukar ba a janye takunkuman da Amurka ta kakaba mata ba.
cigaba ... -
nukiliya : Martanin Zarif Ga Kasashen Turai Game Da Matakin Da Iran Ta Dauka
Faburairu 13, 2021 - 3:27 PMMinistan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bukaci kasashen turai wadanda suka rage a yarjejeniyar nukiliyar kasar dasu karanci kudiri mai lamba 36 kwamitin tsaron MDD game da da yarjejeniyar ta 2015, da wasu wasiku da Iran ta aike kan wannan batun kafin su kai ga babatu game da matakan da Iran ke dauka a baya baya nan.
cigaba ... -
Iran : Har Yanzu Amurka Ba Ta Nuna Da Gaske Ta Ke Ba_Ruhani
Faburairu 12, 2021 - 5:26 PMShugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya bayyana cewa har yanzu sabuwar gwamnatin Amurka ba ta nuna da gaske ta ke yi ba, game da batutuwan da suka shafi Iran.
cigaba ... -
Rauhani: A Cikin Shekaru 42 Iran Ta Yi Nasarar Jure Wa Matsin Lamabar Amurka
Faburairu 11, 2021 - 4:36 PMShugaba Hassan Rauhani na Iran ya bayyana cewa, kasar Iran ta samu nasarar jure wa takunkumai da matsin lambar Amurka.
cigaba ... -
Iran: Cikar Shekaru 42 Da Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci
Faburairu 11, 2021 - 4:32 PMAn Fara Gudanar Da Jerin Gwanon Babrura Na Tunawa Da Ranar Cin Nasarar Juyin Musulunci A Iran
cigaba ... -
Ministan Tsaron Iran Ya Ce: Dukkanin Wadanda Su Ka Yi Fatan Rushewar Juyin Musulunci Sun Ci Kasa
Faburairu 11, 2021 - 4:30 PMMinistan Tsaron Iran Ya Ce: Dukkanin Wadanda Su Ka Yi Fatan Rushewar Juyin Musulunci Sun Ci Kasa
cigaba ... -
Ra’isy: Za A Dauki Fansar Shahadar Sulaimani Abu Mahadi Muhandis
Faburairu 9, 2021 - 4:21 PMBabban alkalin alkalan Iran, Ibrahim Ra’isy wanda ya isa birnin Bagadaza domin ziyarar aiki ne bayyana cewa; Tabbas za a dauki fansar kisan da Amurka ta yi wa Kassim Sulaimani da Abu Mahdi al-Muhandis.
cigaba ... -
Iran Ba Za Ta Mutunta Yarjejeniyar Nukiliya Ba, Har Sai Amurka Ta Janye Mata Takunkumi
Faburairu 8, 2021 - 3:50 PMJagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa, Iran za ta dakatar da matakan da ta dauka kan yarjejeniyar nukiliya ne idan Amurka, ta janye mata gabadayen takunkuman data kakaba mata.
cigaba ... -
Iran:Manzon MDD Kan Rikicin Yemen Ya Gana Da Babban Mai Bawa Ministan Harkokin Wajen Iran Shawara
Faburairu 8, 2021 - 3:47 PMBabban mai bawa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara kan lamuran kasa da kasa Asgar Khaji ya gana da manzon MDD na musamman a kasar Yemen.
cigaba ... -
Iran Ta Shaida Wa MDD, Cewa Ba Zata Lamunci Barazanar Isra’ila Ba
Faburairu 8, 2021 - 3:45 PMIran, ta bayyana wa MDD, cewa ba za ta lamunci duk wata irin barazana ba daga Isra’ila.
cigaba ... -
Iran: Ana Ci Gaba Da Tarukan Cikar Shekaru 42 Na Samun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci
Faburairu 7, 2021 - 4:06 PMDaga cikin muhimman ayyukan da marigayi Imam Khomeni ya gudanar a lokacin rayuwarsa har da kokarinsa na ganin an samu hadin kai tsakanin musulmi.
cigaba ... -
Zarif: Amurka Na Fuskantar Manyan Matsaloli Na Cikin Gida Wadanda Trump Ya Haifar Musu
Faburairu 7, 2021 - 4:06 PMMinistan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, gwamnatin Joe Biden tana fuskantar mayan matsaloli a cikin gida wadanda Donald Trump ya haifar musu.
cigaba ... -
Rouhani: Hukuncin Kotun Duniya Ya Tabbatar Da Ƙarfin Al’ummar Iran Kan Babakeren Amurka
Faburairu 6, 2021 - 5:59 PMShugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya bayyana hukuncin da babban kotun duniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta fitar kan Amurka a matsayin wata nasara ga al’ummar Iran yana mai bayyana hakan a matsayin alamar da ke nuni da nasara da ƙarfin al’ummar Iran ɗin a kan Amurka.
cigaba ... -
Jagora:Ba Abinda Makiya Jumhuriyar Musulunci Ta Iran Suka Iya Da Ita
Faburairu 4, 2021 - 4:34 PMJagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa makiyan JMI, ba abinda suka iya da ita.Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye-shiyenta da harshen larabci a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadar haka a safiyar yau Laraba, a cikin Husainiyyar Imam Khomaini (q) inda ya yi jawabi ga masu rera wakokin yabon iyalan gidan manzon Allah(s).
cigaba ... -
An Gana Tsakanin Ministan Tsaron Kasar Iran Da Babban Hafsan Sojojin Kasar Indiya
Faburairu 4, 2021 - 4:15 PMMinistan tsaro na kasar Iran Burgediya Janar Amir Khatami ya gana da babban hafsan sojojin kasar Indiya a safiyar yau Laraba a gefen taron kasuwar baje kolin kayakin jiragen sama na kasar India.
cigaba ... -
Allah Ya yi wa Farfesa Dahiru Yahaya Rasuwa, Sakamakon Rashin Lafiya
Faburairu 4, 2021 - 4:14 PMRahotanni daga birnin Kano, Nijeriya sun bayyana cewar Allah Ya yi wa sahararren masani kana malamin jami’a, Farfesa Dahiru Yahaya rasuwa yana da shekaru 75 a duniya bayan rashin lafiya da yayi fama da shi.
cigaba ...