Ana Zaman Makoki a Turkiyya Bayan Harin Ta'addanci

  • Lambar Labari†: 797513
  • Taska : VOA
Brief

Hukumomin Turkiyya sun ayyana fara zaman makoki, kwana guda bayan da wasu tagwayen bama-bamai suka tashi a Istanbul, inda akalla mutane 38 su ka rasa rayukansu, kana wasu da dama suka jikkata.

A yammacin Asabar hare-haren suka auku a filin wasan kwallon kafa bayan da aka kammala wani wasa.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce hare-haren sun kaikaici jami’an tsaro ne.

Minisitan cikin gida Suleyman Soylu ya ce 30 daga cikin wadanda suka mutu duk ‘yan sanda ne, sannan sauran fararen hula ne, da kuma wani mutum da ba a gane ko wanene ba.

Hukumomi sun ce hare-haren sun kaikaci wata motar bus ce da ke dauke da ‘yan sanda.

Ya zuwa yanzu babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.

Amma mataimakin Firai ministan kasar ta Turkiyya Numan Kurtulmus, ya ce ga dukkan alamu kungiyar PKK da aka haramta ce ta kai wannan hari.

Kuma ya zuwa yanzu an kama mutane 13 da ake zargin su na da hanu a hare-haren.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky