Turkiyya Ta Jingine Bayanin Cewa Yaro Ne Ya Kai Harin Kunar Bakin Wake

  • Lambar Labari†: 773918
  • Taska : Voa
Brief

Kasar Turkiyya ta jingine bayaninta na farko mai cewa, wani yaro dan kunar baki wake da ISIS ta turo ne ya kai harin nan na ranar Asabar, a wajen wani bikin auren Kurdawa, wanda ya hallaka mutane 54.

Firaminsta Binali Yildrim ya fadi jiya Litini cewa, rade-radin nan na wai wani yaro ne ya kai harin, jita-jita ce kawai daga wasu shaidu.

"Ba mu da masaniya game da wadanda su ka kai harin. Abin takaici, bayanan farko kan wanda ya kai harin da kuma kungiyar da ta turo shi ba daidai ba ne," a bin da ya gaya ma manema labarai kenan.

Da farko Shugaba Recep Tayyib Erdogan ya bayyana maharin da yaro dan shekaru tsakanin 12 da 14, wanda ISIS ta turo. Kusan dukkannin wadanda abin ya rutsa da su Kurdawa ne 'yan kasa da shekaru 18.

Babu wanda ya dau alhakin kai harin, to amma salon harin da kuma irin bam din da aka yi amfani da shi na da kamanni da hare-haren da ISIS ta kai a baya.

Maharin ya auna wani bikin auren Kurdawa ne a Gaziantep, wani birnin da bai wuce nisan kilomita 60 ba daga arewacin Siriya, wanda kuma ke kunshe da al'ummar 'yan gudun hijira, wadanda su ka guje ma yakin basasar Siriya.

Jiya Litini Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ce kasarsa ta lashi tokobin kakkabe ISIS kwata-kwata daga iyakarta da Siriya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky