Gwamnatin Turkiya ta bada umurnin kame tsohon dan wasan kwallon kafar kasar

  • Lambar Labari†: 771659
  • Taska : RFI
Brief

Gwamnatin Turkiya ta bada umurnin kame tsohon shahararren dan wasan kwallon kafar kasar, kuma a yanzu dan majalisa a Turkiyyan, Hakan Sukur tare da mahaifinsa Selmet Sukur.

A Juma’ar da ta gabata hukumomin tsaron kasar suka zargi Hakan Sukur da mahaifinsa Selmet Sukur da zama manbobin kungiyar Fethulla Gulen wanda aka zarga da kitsa yunkurin juyin mulkin da bai yi nasaraba a kasar.

Sai dai rahotanni sun ce jami’an tsaro basu samu Hakan Sukur da mahifinsa ba a gidajensu dake Istanbul kasancewar sun fice daga kasar tun a shekarar da ta gabata, ana kuma zaton sun samu mafaka a kasar Amurka.

Hakan Sukur yayi suna sosai a fagen kwallon kafar kasar Turkiya saboda gagarumar gudunmawarsa, musamman a gasar cin kofin duniya ta 2002, kafin daga bisani ya zama dan majalisar kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky