Za a sanya wa masallatai takunkumi a Faransa

  • Lambar Labari†: 768712
  • Taska : BBC.COM
Brief

Firai Ministan Faransa, Manuel Valls, ya ce yana duba yiwuwar dakatar da masallatan kasar daga karbar taimakon kudi daga kasashen waje.

Mista Valls ya bayyana haka ne bayan jerin hare-haren da ake zargin masu fafutikar Jihadi ne suka kai wa kasar a kwanakin baya bayan nan.

Firai Ministan ya shaida wa jaridar Le Monde newspaper cewa ya yi kira ga dukkan limaman masallatan kasar su rika neman karin ilimin addini a cikin kasar ba sai sun fita waje ba.

Ya ce lokaci ya yi da Faransa za ta sabunta "dangantakarta da Musulinci", yana mai cewa yanzu kasar za ta bai wa yaki da tsattsauran ra'ayin addini fifiko.

Gwamnatin kasar dai na ci gaba da shan suka a kan gazawarta ta hana kai manyan hare-hare uku a cikin wata 18.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni