Musulmin Birtaniya Sun Damu Kan Matsayin Da Aka Baiwa Thereza Na Firayi Minista

  • Lambar Labari†: 765928
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Da dama daga cikin muslmin kasar Birtniya sun fara nuna damuwa dangane da matsayin firayi minista da aka baiwa Theresa May saboda ra’ayinta na ‘yan mazan jiya.

Tun bayan da Margaret Thatcher ta rike matsayin firayi minista a kasar Birtaniya shekaru 26 da suka gabata, Theresa May ta sake zama mace ta biyu a kan wannan matsayi.

David Cameron ya sanar da cewa zai yi murabus daga kan mukaminsa ne tun bayan da kasar ta kada kuri’ar raba gardama kan ficewa daga kungiyar tarayyar turai.

Wannan ya bayar da dama ga masu tsatsauran ra’ayin yan mazana jiya domin su sake rike madafun iko a kasar, domin kuwa a halin yanzu kasar ta fice daga kungiyar tarayyar da suke kallonta a matsayin wani karfen kafa na hana su cimma manufofinsu.

Babban abin da musulmi suke fargaba a kansa dangane sake dawowar masu tsatsauran ra’ayin yan mazan jiya shi ne, yadda suke nuna kyama ga wasu bangarorii da ba yan asalin kasar ba, musamman ma mabiya addinin muslunci wadanda akasarinsu yan kasashen ketare ne.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky