An Kashe Wani Dan Najeriya A Kasar Italiya

  • Lambar Labari†: 764649
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Magajin garin Fermo dake kasar Italiya ya da kashe wani Dan Najeriya

jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta nakalto Paolo Calcinaro magajin garin Ferno dake tsakiyar Italiya a wananLaraba na cewa wani dan bindiga daga cikin masu gyamar baki ya buda wuta a kan Emmanuel Chidi wani Dan Najeriya mai shekaru 36 a Duniya da ya nemi mafuka a kasar, inda ya samu mumunar rauni bayan kuma an garzaya da shi asibiti ya cika.

Mista Calcinaro ya ce watanni takwas da suka gabata,Emmanuel Chidi yana zaune ne a wani sansani na 'yan gudun hijra dake kalkashin Majami'ar Katolika mai suna Caritas dake cikin garin na Ferno.

Daga farkon wannan shekara ta 2016 wato cikin watanni shida da suka gabata, kimanin 'yan gudun Hijra dubu 71 ne suka shiga kasar Italiyan ta hanyar Ruwan Bahrmu kuma mafi yawan su 'yan kasashen Afirka da gabas ta tsakiya ne.

Duk da irin hadarin dake tattare a hanyar na zuwa kasashen Turan, inda dubai suke rasa rayukansu a hanya, to amma duk da haka bakin hauren na ci gaba da kwarara zuwa Turan domin neman rayuwa mai kyau.

Yanzu haka Kasashen na Turai na ci gaba da tuntubar wasu kasashen Afirka da na gabas ta tsakiya kan yadda za a magance wannan matsala.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky