Dan ta'adda ya kusan hallaka fitattun mutane a Faransa

  • Lambar Labari†: 760383
  • Taska : RFI
Brief

Hukumomin Faransa sun ce, dan ta’addan nan da aka kashe bayan ya hallaka wani dan sanda da abokiyar zamansa, na dauke da jerin sunayen wasu fitattun mutane da zai kai wa hari, cikin su har da 'yan Jaridu.

Mai gabatar da kara a kasar Faransa Francois Mollins ya ce, 'yan sanda sun sami jerin sunayen mutanen da aka shirya kai wa hari a kusa da inda Larossi Abballa ya kashe Jean Baptiste Salvaing da abokiyar zamansa Jessica Schneider.

Mollins ya ce, jerin sunayen sun kunshi manyan mutane da kuma 'yan jaridu da mawaka da kuma bukatar ganin sun mayar da gasar cin kofin kwallon Turai da ake gudanawar ya koma zaman makoki.

'Yan sandan sun ce, sun gano wukake guda uku a inda ya kai harin kuma daya daga cikinsu dauke ta ke da jini.

Mai gabatar da karan ya ce, yanzu haka an kama wasu matasa uku da ke tafiya tare da Abballa kuma daya daga cikinsu na daga cikin wadanda aka daure a shekarar 2013 saboda samun su da laifin kokarin dibar sojan gona zuwa Pakistan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky