An Samu Sabanin Fahimta Tsakanin Faransa da HK Isra'ila

  • Lambar Labari†: 754641
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Gwamnatin Faransa ta yi watsi da zargin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi wa kasar na goyan bayan Falasdinawa akan shirin sasanta rikicinsu da Israila da take shiryawa.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Marc Ayrault ne ya yi watsi da furucin na Netanyahu wanda ke zargin cewar goyan bayan da Faransa ta bai wa hukumar UNESCO wadda ta amince da halascin Falasdinu, nuna kiyayya ce ga Israila.

Ayrault ya ce Faransa za ta ci gaba da taka rawa wajen ganin an samo masalaha kan takaddamar da ke tsakanin Yahudawa da Falasdinawa bayan ya gana da firaminista Benjamin Netanyahu da shugaba Mahmud Abbas.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky