'Yan sandan Brussels sun cafke mutane 6

  • Lambar Labari†: 743039
  • Taska : BBC
Brief

'Yan sanda a kasar Belgium sun kama mutane shida a cigaba da samamen da suke kai wa bayan hare-haren da aka kai birnin Brussels da ya hallaka mutane sama da talatin.

An yi kamen a ciki da wajen gundumomin birnin Brussels, da binciken kowacce gida a kokarin da suke yi na gano wadanda ake zargi da hannu a kai harin.

Sai dai 'yan sanda ba su bayyana sunayen wadanda suke tsare da su ba, a bangare guda kuma jami'an tsaro sun gano wasu mutane biyu da ake zargin sun gudu bayan kai harin.

An dai gano su ne a hotunan internet tare da wanda ake zargi a filin jirgin sama da tashar jirgin kasa wuraren da bama-baman suka ta shi.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky