Bama-Bamai Sun Fashe A Filin Jirgin saman Birnin Brussels

  • Lambar Labari†: 742604
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Wasu Bama-Bamai Sun Fashe A Filin Jirgin saman Birnin Brussels, Na Kasar Belgium.

Rahotanni daga kasar Belgium sun bayyana cewar wasu bama bamai guda biyu sun fashe a filin jirgin sama na Zaventem da tashar jirgin kasa na Malbeek da ke birnin Brussels, babban birnin kasar Belgium din, inda wasu rahotanni suka ce alal akalla mutane 13 sun mutu wasu da dama kuma sun sami raunuka.

Kafafen watsa labaran kasar sun bam na farko dai ya fashe a filin jirgin saman da misalin karfe na 8 na safe lokacin kasar, kana kuma bayan wasu 'yan mintuna aka ji fashewar na biyu a tashar jigin kasa na karkashin kasa kusa da helkwatar kungiyar Tarayyar Turai da ke birnin na Brussels, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 13 kana wasu 35 kuma suka sami raunuka wasun ma cikin mawuyacin hali.

Wasu kafafen watsa labaran dai sun ce kafin fashewar bama-baman dai an ji karar harbe harben bindiga da kuma muryar wasu mutane da aka ce suna larabci.

Tuni dai aka rufe filin jirgin saman na Brussels da kuma daukar tsauraran matakan tsaro a duk fadin garin; kamar yadda wasu kasashen Turan ma suka sanar da daukan karin matakan tsaro.

Wadannan hare-hare dai sun zo ne 'yan kwanaki bayan da jami'an tsaron kasar ta Belgium suka kama Salah Abdeslam, wanda ake zargi da kitsa hare haren da ta'addancin da aka kai birnin Paris na kasar Faransa a watan Nuwamban bara.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky