Paris: 'Yan sanda sun kama Salah Abdeslam

  • Lambar Labari†: 741916
  • Taska : bbc
Brief

Rahotanni da ake samu da dumi-dumin sa na cewa, 'yan sanda sun bayar da tabbacin cewa Salah Abdeslam ya samu rauni a wani samame da suka kai a garin Molenbeek, da ke birnin Brussels.

An yi musayar wuta lokacin da 'yan sandan Belgium suka kai samame a unguwar, inda rahotanni ke cewa akalla mutum daya raunata, a yayin da jami'an tsaro ke neman Salah Abdeslam ruwa a jallo, wanda ake zargi na da hannu a harin da aka kai birnin Paris a watan Nuwamban da ya wuce.

Daga farko dai masu shigar da kara sun ce, an samu hoton yatsun Salah Abdeslam a wani gida a Brussels, inda 'yan sanda suka kai samame ranar Talatar da ta gabata.

Jami'an tsaron sun ce ana zaton ya tsere lokacin da aka kai samamen, yayin da aka kashe wani dan bindiga mai suna Mohamed Belkaid.

A watan Nuwamban shekarar 2015 ne 'yan bindiga suka kai hari birnin Paris, inda suka kashe mutane 130.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky