Rasha Ta Fara Gudanar Da Atisayin Soji

  • Lambar Labari†: 734000
  • Taska : HAUSA.IR
Brief

Ministan Tsaron kasar Rasha ya sanar da fara Atisayin Soja A yau Litinin.

Mista Sergueï Choïgou ya ce wannan Atisaye na zuwa ne bisa umarnin shugaban kasar ta Rasha Vilaminin Putin ya bayar, kuma manufar wannan Atisayi karfafa matsakan tsaro tare da shirin ko ta kwana a yankunan kudancin kasar

An fara Atisayin ne a safiyar yau Litinin,inda Dakarun tsaro na kasa da sama suka fara gwada irin kwarewar da suke da.

Masu sharhi kan harakokin tsaro na ganin wannan Atisayi a matsayin gwada irin karfin da Rasha keda a bangaran tsaro musaman ma wajen tunkarar barzanar kungiyar Tano.

A shekaru biyun da suka gabata sabani ya shiga tsakanin kungiyar Tano da Rasha sanadiyar rikicin kasar Ukreine, kuma a 'yan kwanakin nan rikicin ya kara kamari sanadiyar rikicin kasar Siriya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky