kasashen Amurka,saudiya da Burtaniya sun yi ganawar sirri .

  • Lambar Labari†: 730597
  • Taska : HAUSA.IR
Brief

ministocin kasashen Amurka,saudiya da Burtaniya sun yi ganawar sirri.

A jiya Alkhamis, ministan harakokin wajen Amurka Jen Kery da Adil Aljubair na saudiya tare da Philip Hammond na kasar Burtaniya sun gudanar da wata tattaunawa a birnin London na kasar Burtaniya

duk da cewa an gudanar da tattaunawar ce cikin sirri, saidai masu sharhi na ganin cewa tattunawar ba ta rasa nasaba kan abinda ke faruwa a yankin gabas ta tsakiya musaman ma dangane da yanke alakar diplomasiya da kasar Saudiya ta yi da jamhoriyar musulinci ta Iran.

a baya dai kasar Amurka ta baiwa masarautar Al'sa'oud tabbacin goyon bayanta, musaman kan batun da ya shafi rikicin kasar Siriya da kasar Yemen.

bayan Amukra, Burtaniya ita ce kasar ta biyu da take sayar kasar Saudiya makamai,a baya bayan nan kungiyoyin kasa da kasa sun bayyana cewa mafi yawan makaman da kasar Saudiya ta yi amfani da su wajen rusa kasar Yemen da kisan karen dangi da take yiwa Al'ummar kasar yemen na kasar Burtaniya ne.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky