Rasha ta yi watsi da rahoton Amnesty na kashe mutane

  • Lambar Labari†: 726609
  • Taska : RFI
Brief

Gwamnatin Rasha ta yi watsi da rahotan Kungiyar kare hakkin bil ‘adama ta Amnesty International da ke cewa kasar ta kashe daruruwan fararen hula a hare haren saman da ta ke kai wa a Syria. Rasha ta ce an shirya rahotan ne domin yi mata kazafi.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce bayan gudanar da dogon bincike da nazari kan rahotan Amnesty, ta fahimci cewa babu kamshin gaskiya a rahotan, face karerayi da kazafi da aka saba yi wa kasar.

A cewar mai magana a madadin ma’aikatar tsaron Igor Kona-shen-kov, Amnesty tana musun cewa, hare haren da Rasha ke kai wa ba kan ‘yan ta’adda suke zuwa ba, al halin ba ta da hanyar gano haka.

A jiya laraba ne kungiyar, ta fitar da rahotan da ke bayyana yadda ake kashe fararan hula a hare-hare da Rasha ke kaddamarwa a Syria da Iraqi, yayin da Amnesty ta ce hakan ba shi da maraba da aikata laifukan yaki.

Amnesty ta kuma ce tana da shaidun da ke nuna cewa Rasha na amfani da bama-baman da aka haramta wajen kai hari a masallatai da asibitoci

Yayin da Rasha ta sake jaddada matsayinta tare da sukan rahotan da ta ce, ba shi da wata hujjar da za a dogara da ita, kuma hare-harenta na zuwa ne kan mayakan IS.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky