Tarayyar Turai ta tsawaitawa Rasha takunkumi

  • Lambar Labari†: 726279
  • Taska : rfi
Brief

Kungiyar Tarayyar Turai ta tsawaita takunkuman kariyar tattalin arziki da ta kakaba wa Rasha sakamakon rawar da kasar ke takawa a rikcin Ukraine.

Mambobin Kasashe 28 a majalisar kungiyar wadanda suka gudanar da taro a birnin Brussels, sun ce Rasha ta ki mutunta yarjejeniyar sulhun da aka kulla tsakaninta da Ukraine da kuma ‘yan aware a birnin Minsk domin kawo karshen wannan rikici, saboda haka ya zama wajibi a tsawaita takunkuman da aka sanya wa kasar.

Kungiyar Turai ta ce ta lura shekara ta 2015 na gaf da kawo karshe ba tare da Rasha ta canza matsayi a game da irin rawar da ta ke takawa a gabashin Ukraine ba, kuma a irin wannan yanayi ba makawa face tsawaita takunkuman karya tattalin arziki a kanta.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar jim kadan bayan sanar da matakin na Tarayyar Turai, ma’aikatar harkokin wajen Rasha, ta bayyana takaicinta a game da yadda kungiyar ta kawar da kai a game da matsalar ta’addanci wadda ita ce babbar barazana a cewarta, inda a maimakon haka Turai ta zabi tsawaita takunkuman.

Kafin nan dai Firaministan Rasha Dmitry Medvedev, ya ce za su tsawaita takunkumai na tattalin arziki a kan kasar Ukraine saboda kasar ta zabi yin huldar kasuwanci da Turai a maimakon Rasha.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky