‘yan sanda da sojoji dubu 120 ne aka tanada domin kawo tsaro a zabe Faransa

  • Lambar Labari†: 723342
  • Taska : RFI
Brief

An baza dubban ‘Yan sanda da sojoji a karkashin dokar ta baci da aka kafa a kasar Fransa domin tabbatar da tsaron rumfunan zaben manyan yankunan kasar Fransa, inda aka kara daukar tsaurara matakan tsaro ga birnin Paris da a baya ya shiga zaman makoki, sakamakon mutuwar mutane 129 a cikin harin ta addancin ranar 13 ga watan november da ya gabata a birnin na Paris.

Tsakanin jandarmomi, ‘yan sanda da kuma sojoji, dubu 110 000 zuwa dubu 120 000 ne, aka banza a ko wane lungu da sako na kasar ta Fransa, domin gudanar da aikin tabbatar da tsaron ganin, zaben ya gudana cikin tsaro da kwanciyar hanakali, sakamakon barazanar da kasar ke fuskanta na kara kai mata hare haren ta addanci, daga kungiyar Isis, da ta dau nauyin harin farko da ya jefa kasar cikin yaki a yankin gabas ta tsakkiya da mayakan na Isis.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni