Jamus ta shiga sahun yaki da kungiyar ISIS a Syria

  • Lambar Labari†: 723000
  • Taska : RFI
Brief

Majalisar dokokin Jamus ta amince da shiga yakin da ake yi da kungiyar ISIS a kasar Syria bayan ta kada kuri’a a yau jumma’a, inda mambobinta 445 suka goyi bayan haka yayin da 146 suka nuna rashin amincewarsu.

Yanzu haka Jamus za ta aika jiragen yaki da suka hada da na sama da ruwa da kuma dakaru 1,200 zuwa Syria, amma ana zaton dakarun ba za su shiga fada gaba da gaba da ISIS ba.

Wannan matakin na zuwa ne bayan kasar Faransa ta bukaci taimakon manyan kasashen duniya sakamon hare haren ta’addancin da ISIS ta kaddamar ma ta a watan jiya tare da kashe mutane 130.

A jiya Alhamis ne jiragen yakin Birtaniya suka kai hare haren sama kan mayakan ISIS a Syria bayan majalisar dokokin Birtaniya ta amince da haka.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky