Mutane 6,000 za su yi zanga zanga a Madrid

  • Lambar Labari†: 721554
  • Taska : IFR
Brief

Fitattun masu shirin fina finan kasar Spain tare da 'yan Jaridu da kuma 'yan siyasa 6,000 sun bukaci gudanar da zanga zangar lumana a karshen wannan makon a birnin Madrid don nuna adawa da yadda kasashen duniya ke amfani da karfi sakamakon harin da aka kai birnin Paris.

Wata sanarwa da Magajin garin Barcelona Ada Colau da Pilar Barden mai shirin fina finai da kuma Chechu Monzon mai gabatar da shirye shirye a talabijin din kasar suka sanyawa hannu tare da mutane sama da 6,000 ta bayyana cewar basa goyan bayan karawar da ake tsakanin 'yanci da tsaro.

Sanarwar ta ce, idan mayar da martani kan harin ta’addanci ya bukaci kawar da 'yancin bil Adama, hana walwala da kuma tilasta wa jama’a zama a gida, to lallai ta’addanci ya samu nasara.

Sanarwar ta bukaci gudanar da zanga zangar  a ranar Asabar da karfe 12 na rana a Madrid don nuna rashin amince wa da munanan hare haren da ake kai wa kan fararen hula a Syria.

Sanarwar ta kara da cewa halayyar wasu 'yan mutane kadan bai dace ya zama dalilan afka wa daukacin al’umma ba.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky