Harin ta'addancin ya kashe sama da mutane 120 a birnin Paris

  • Lambar Labari†: 719812
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

A birnin Paris na Faransa akalla mutane 120 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta’addancin da ake kai wa birnin a cikin daren juma’ar da ta gabata.

Da farko an samu fashewar bama-bamai har sau uku a wajen filin Wasa na Faransa, yayin da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da gidan wasa na Bataclan inda a can kawai aka samu asarar rayukan mutane 80.

Daga bisani dai an yi musayar harbe-harbe tsakanin ‘yan wasa da kuma ‘yan bindiga. Shugaban Faransa Francois Hollande na ayyaka kafa dokat ta baci a kasar, yayin da aka bayar da umurnin rufe illahirin iyakokin kasar baki daya.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe daya na daren da ya gabata, kuma binciken farko da jami’an tsaron suka gudanar ya tabbatar da cewa yawan maharan zai kai 8.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky