EU ta caccaki Turkiya kan hakkin dan Adam

  • Lambar Labari†: 719338
  • Taska : http://www.dw.com/ha
Brief

Kungiar Gamayyar Turai ta fitar da rahoto da ya soki lamarin Turkiya dangane da al'amuran da suka shafi kare hakkin bil adama da kuma fadin albarkacin baki

Cikin rahoton da suka wallafa a wannan Talatar, hukumomin Bruxelles sun bayyana cewar a shekarar da ta gabata Turkiya ta yi katsalandan a harkokin da suka shafi shar'ia da kuma aikin jarida da kuma na 'yancin gudanar da taro.

Tun a watan Oktoba ne ya kamata EU ta fitar da wannan rahoto da ke nazari kan sharudan da Turkiya ya kamata ta cika domin samun damar shiga cikin kungiyar gamayyar Turai, amma kuma aka dageshi sakamakon zaben 'yan majalisa da aka gudanar a kasar da kuma matsalar kwararar 'yan gudun hijirar Syriya.

Kungiyar ta Tarayyar ta yi kira ga fadar mulki ta Ankara da ta zauna kan teburin tattaunawa da Kurdawa domin dinke barakar aware da ke tsakaninsu idan ta na so ta shiga cikin EU. Sannan kuma ta nemi Turkiya ta sakarwa fannin shari'a da kuma kafafon watsa labarai marar gudanar da aikinsu ba tare da tsangwama ba. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni