Masu bincike sun yi amannar bom ne ya tarwatse jirgin Rasha

  • Lambar Labari†: 719203
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Kashi 90 cikin dari na Masu binciken hatsarin jirgin saman Rasha da ya kashe mutane 224 a sararin samaniyar kasar Masar, sun yi amannar cewa bam ne ya yi sanadiyyar fadowar jirgin a yankin Sinai.

Masu binciken sun ce akwai kara mai kama da fashewar bom da aka ji daga na’urar da ke nadar bayanai a jirgin.

Jirgin dai ya tarwatse ne bayan tashinsa minti 23 daga tashar Sharm al Sheikh a Masar a ranar Asabar karshen makon jiya. Kuma tuni mayakan IS da ke da’awar jihadi suka yi ikirarin daukar alhakin tarwatsewar jirgin.

Hasashen da ake bom ne ya tarwatse jirgin, ya sa baki ‘yan yawon bude na gaggawar ficewa Masar. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky