Rasha za ta tura jirage 44 domin kwaso ‘Yan kasarta a Masar

  • Lambar Labari†: 719054
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Gwamnatin Rasha tace za ta tura jirage kimanin 44 domin kwaso ‘Yan kasarta da suka je yawaon bude a Masar, a yayin da ake ci gaba da fargaba akan bom ne ya yi sanadin hatsarin jirgin kasar dauke da fasinja 224.

Rahotanni sun ce ‘Yan Rasha da Birtaniya sun makale a tashar Sharm el Shiekh bayan Rasha ta bayyana dakatar da jigila zuwa Masar a ranar Juma’a.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake fargaba akan zargin bom ne ya tarwatse jirgin Rasha dauke fasinjan da ke cikinsa 224 a ranar 31 ga watan Oktoba.

Rasha tace ‘yan yawon bude idon na iya dawo wa a lokacin da suka ga dama, amma babu wani tsari na kwaso su cikin gaggawa.

Gwamnatin Masar kuma ta yi watsi da zargin bom ne ya yi sanadin faduwar jirgin fasinjan na Rasha, inda ta ce bincikenta har yanzu bai tabbatar da Bom ne. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky