Wani jirgin saman Rasha ya fadi a kasar Masar

  • Lambar Labari†: 718048
  • Taska : voahausa.com
Brief

Jiya Asabar wani jirgin saman fasinja na kasar Rasha ya fadi a zinrin Sinai, ya kashe dukkan mutane maitan da ashirin da hudu da suke cikin jirgin.

Jiya Asabar wani jirgin saman fasinja na kasar Rasha ya fadi a zinrin Sinai, ya kashe dukkan mutane maitan da ashirin da hudu da suke cikin jirgin.


Kusan dukkan fasinjojin yan kasar Rasha ne yan yawon bude ido, wadanda suke komawa Saint Petersburgh daga wurin shakatawar kasar Masar na Sham El Sheikh. Wasu yan kasar Ukraine guda uku suna daga cikin wadanda suka mutu.


Ya zuwa yanzu dai masu aikin gaggawa sun zakulo gawrwarkin akalla mutane dari da ashirin da tara, tare da na'urorin jirgin da ake cewa black boxes da turanci da suka dauki bayanin harkokin jirgin ciki harda maganganun da aka yi tsakani matuka jirgin

.
Masana zirga zirgan jiragen sama sun baiyana fatar bayanan na'urorin zasu basu bayanan abubuwan da suka sa jirgin ya fadi.


Kingiyar Islamic State a kasar Masar tayi ikirarin cewa ita keda alhakin harbo jirgin. To amma masana sufurin jiragen sama dana soja sun ce hakan ba zai yiwuwa ba. Domin sunce jirgin yana tafiyar mita dubu dara da dari daya tsakaninsa da kasa kafin ya fadi, kuma kungiyar ISIS bata da makamai masu linzami da za'a harba na wannan nisa

.
Jmi'in lura da zirga zirgan jiragen sama na kasar masar Hossan Kamal yace binciken jirgin da aka yi kafin ya tashi bai gano wata matsala ba, kuma matukin jirgin bai bada wani bayani kafin jirgin ya bace ba.
Shugaban Rasha Vladim Putin ya ayyana yau Lahadi a zaman ranar makoki a duk fadin kasar sa


Shi kuma sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry wanda ya fara ziyara a tsakiyar Asiya ya yiwa Rasha ta'aziya. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky