Turai ta cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

  • Lambar Labari†: 715356
  • Taska : bbc.com/hausa
Brief

Shugabannin tarayyar turai da suke tattaunawa a Brussels sun ce sun cimma matsaya kan shirin da suke yi na neman tallafin kasar Turkiyya da nufin magance matsalar shigar masu gudun hijra zuwa turai.

Shugaban hukumar tarayyar turai, Jean-Claude Juncker ya ce yanzu haka Turkiyya ta yarda da ta hana 'yan hijrar dake kasarta kwarara zuwa turai akan tsarin ban gishiri in ba ka manda.

Ita kuma a nata bangaren tarayyar ta turai ta alkawarta wa Turkiyyar samun biza ga 'yan kasarta da za ta ba su damar mazayawa a nahiyar turai ba tare da tsangwama ba.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da cewa tarayyar ta turai tana duba yiwuwar ba wa Turkiyyar tallafin Yuro biliyan uku domin daukar dawainiyar 'yan gudun hijrar kasar Syria da ke zaune a Turkiyyar. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky