'Yan gudun hijira na cigaba da shiga Turai

  • Lambar Labari†: 712167
  • Taska : dw.com/ha
Brief

Dubban 'yan gudun hijira ne ke cigaba da shiga Turai daidai lokacin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci a magance abubuwan da ke sanya gudun hijira.

Hukumomi a Hungary suka ce mutane sama da dubu goma ne suka shiga kasar ta cikin Croatia yayin da a Austria aka bada labarin shigar 'yan gudun hijira sama da dubu takwas a cikin sa'o'i talatin da shidddan da suka gabata.

Galibin mutanen da suka shiga kasashen dai sun fito ne daga Siriya wadda a yanzu haka ke fama da yakin basasa wanda ya yi sanadin rasuwar dubban mutane.

A wani taro da suka kammala dazu, shugabannin kasashen Turai sun amince da kara kudin tallafin da aka saba badawa ga kasashen da ke makotaka da Siriya a wani mataki na rage yawan wanda ke barin yankin don neman mafaka a Turai. 289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni