Shugaban hukumar kare hakkokin Bil Adama ta MDD ya yi kiran samar da tsari ga' yan gudun hijira

  • Lambar Labari†: 710744
  • Taska : dw.com/ha
Brief

Zeid Ra'ad Al Hussein ya bukaci nahiyar Turai da sauran kasashen duniya da su samar da nagartaccen tsari kan tafiyar da matsalolin 'yan gudun hijira.

A yayin bude taron hukumar karo na 30 a birnin Geneva Shugaban hukumar kare hakkokin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein ya jaddada kudirin hukumar na ganin mahukuntan Afirka da Amirka da yankin Asiya gami da nahiyar Turai daukar kwararan matakai masu inganci domin jin dadin 'yan gudun hijira a duniya.

Kazalika Zeid Ra'ad ya kuma jinjina wa masu zanga-zangar nuna goyan bayan 'yan gudun hijira daga sassan kasashen Tarayyar Turai a bisa yadda suka yi tsayin daka kan halin da 'yan gudun hijirar suka shiga.

Fiye dai da mutane dubu 430,000 'yan gudun hijira da suka ketara zuwa kasashen Turai a wannan shekarar wanda mafi yawancinsu sun fito daga kasashen Larabawa da kuma Afirka.289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky