Hollande ya ce babu ban-banci tsakanin yaki da Boko Haram da ISIS

  • Lambar Labari†: 710742
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Bayan ganawarsu da Shugaban kasar Najeriya Muhamamdu Buhari, Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana cewar babu banbanci tsakanin yaki da kungiyar Boko Haram da mayakan ISIS.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ke ziyarar kwanaki 3 a Faransa ya bukaci taimakon kasar wajen murkushe Boko Haram wanda ta fadada hare haren da take kai wa bayan ta sanar da mubaya’a ga mayakan ISIS.

Shugaba Francois Hollande ya ce suna da masaniyar cewar kungiyar Boko Haram ta kara karfi bayan kulla hulda da ISIS, saboda haka yaki da ita ya zama wajibi kamar yadda ake yi da ISIS, domin babu ban-banci kan ayyukan ta’addancin da suke a tsakanin su.

Wata majiyar fadar shugaban Faransa ta ce ya zuwa yanzu taimakawa Najeriya wajen yakin ya sauya ne kawai wajen bada bayanan asiri.

Yau ake saran shugaban Najeriya zai gana da 'yan kasuwa da masu zuba jari da kuma shugabanin kanfanin Total da Lafarge.289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky