Turai za ta iya magance matsalar 'Yan gudun hijira: MDD

  • Lambar Labari†: 710062
  • Taska : http://ha.rfi.fr
Brief

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisr Dinkin Duniya ta bayyana yakininta na cewa hukumomin Kasashen Turai za su iya magance matsalar kwararar bakin haure.

Wannan na zuwa ne yayin da shugabar Gwamantin Jamus Angela Merkel ta ce Kasashen na Turai na bukatar rarraba dubban bakin haure a tsakaninsu.

Shugaban hukumar dake kula da 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce za a samu karuwar adadin mutanen dake rasa matsugunnansu matukar kasashen duniya suka kau da kai wajan daukan matakan magance matsalolin da ake fama dasu a sassa dabam dabam na duniya.

Guterres ya yi kira da a kara samar da hanyoyin halal domin baiwa bakin haure damar shiga kasashen Turai kai tsaye kuma ya bayyana cewa kimanin bakin haure dubu 5 ne ke shigowa Turai a ko wace rana.

A cewarsa, kawo yanzu bakin haure dubu 300 ne suka tsallaka Tekun Medireeeanean da nufin samun ingantacciyar rayuwa a Turai wadda a jumulce ke da mutanen da yawansu yakai miliyan 508. ABNA289


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky