SHAFIN GLOBAL FIRE YA BAYYANA KASASHE 4 A AFRIKA DA SUKA FI KWAREWA A HARKAR SOJI CIKI HAR DA NIGERIA

  • Lambar Labari†: 708377
  • Taska : AFP
shafin global fire mai yin nazari kan yanayin karfin soji da tsaro a da kowace kasa take da shi a wannan karon ya fitar da rahoto dake nuna cewa kasashen Nigeria Afrika ta kudu, Masar Aljeria a matsayin kasashen da suka fi karfin soji da kwarewa wajen tababtar da tsaro a nahiyar Afrika, A bangaren kasashen turai kuwa ya nuna kasashen Amurka Rasha da China a matsayin na gaba ta fuskar karfin soji da tabbatar da tsaro a duniya baki daya.

 A wani rahoto daya saba fitarwa kowace shekara, shafin Global Fire Power mai nazari kan harkar tsaro da kwarewar sojoji a Duniya ya zayyano kasashen Amurka, Rasha da China daya bayan daya a matsayin wadanda suka fi kwarewa a harkar soji da kayan aiki Duniya.

Shafin ya kuma Ambato kasashen Mali, Mozanbique da Somaliya a mastayin kutal a wannan fani.

Kazalika a nahiyar Afirka rahoto ya zayyano kasashen Masar, Aljeriya, Afirka ta Kudu da Najeriya a mastayin na gaba wajen kayan aiki da kuma kwarewa a sha’anin tsaro da soji.

A wannan rahoto kuma shafin na Global Fire Power ya rawaito Kasar Nijar a matsayi na 10, yayinda kasar Cadi ke matsayi na 12.

 

 


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky