Taron G7 na kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya

  • Lambar Labari†: 694262
  • Taska : rfi
Brief

Shugaban Amurka Barack Obama ya isa kasar Jamus domin halartar taron shugabannin kasashen 7 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7 wanda za a buda a yau lahadi.

Shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel ce dai ta karbi Obama yayin da sauran shugabannin kasashen duniya ke ci gaba da isa a yankin Elmau inda za a gudanar da taron.

Daga nahiyar Afirka ma dai akwai shugabannin da aka gayyata domin halartar wannan taro da ke tattaunawa manyan batutuwa da suka shafi tattalin arziki tsaro da dai sauransu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda ke halatarta taron.288

A nasu bangarori kuwa kungiyoyi masu yaki da tsarin jari hujja na gudanar da zanga-zangar adawa da taron na G7.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky