'Yan Sandan Australia sun gano wani yunkurin ta'addanci a kasar

  • Lambar Labari†: 689054
  • Taska : rfi
Brief

Yau Asabar ‘Yan sandan kasar Australia sun ce sun gano yunkurin da aka yi na kai harin Bom a Melbourne, inda suka kama wani matashi mai shekaru 17, tare da kwance abubuwa masu fashewan da aka dasa.

Mataiamakin Kwamishinan ‘yan sanda Mike Phelan, yace suna zargin matashin da shirin aikata ta’addanci, da kuma mallakar abubuwan dake da alaka da ayyuka irin na ‘yan ta’adda.
‘Yan sandan sun ce sun sami rahotannin dake nuna cewa ana ana shirin kai harin ne a birnin Melbourne gobe Lahadi, da ita ce ranar uwaye a kasar ta Australia.
‘Yan sandan sun ce saboda karancin shekarun wanda ake zargin, ba zasu bayyana sunan shi ba, amma kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya ranar Litinin.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Prophet's birthday celebrations
We are All Zakzaky