Austria ta haramtawa Musulmi samun tallafi

  • Lambar Labari†: 673438
  • Taska : rfi
Brief

Majalisar Kasar Austria ta amince da wata sabuwar dokar hana kungiyoyin Musulmin kasar samun tallafin kudade daga kasashen waje tare da kuma tilastawa Limamai koyan harshen Jamusanci. Wannan sabuwar doka da ministan harkokin cikin gidan Austria Sebastian Kurz ya kira ta a matsayin Musuluncin Turai an yi ta ne don dakile tasirin ra’ayoyin Musulmin kasashen duniya a cikin kasar

Dokar ta kuma kara bai wa al’ummar Musulmin kasar ‘yancin gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ba.

Sai dai dokar ta gamu da suka daga sassa dabam dabam, cikin su har da Musulmin kasar da ke shirin kalubalantar dokar a kotu.

Ko a watan jiya shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci janyo al’ummar Musulmi a jika maimakon yadda ake nuna musu kyama.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky