Rasha ta amince a shata sabon tsarin sasanta rikicin Ukraine

  • Lambar Labari†: 669700
  • Taska : rfi
Brief

Shugabannnin kasashen Rasha da Jamus da Faransa sun amince su samar da wani sabon tsari da zai taimaka a kawo karshen rikicin kasar Ukraine. Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwaranta na Faransa Francios Hollande tare Vladimir Putin na Rasha sun amince da matakin ne bayan sun shafe sa’oi suna ganawa ta musamman a birnin Moscow

Kasashen sun amince su shata matakan kawo karshen rikicin tare da kudirorin da shugaban Ukraine Petro Poroshenko zai gabatar.

Amma babu wani cikakken bayani game da kudirorin da kuma matakan da kasashen zasu dauka domin kawo karshen rikicin na Ukraine da ya lakume rayukan mutane sama da 5,000.ABNA


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky