Wani dan siyasa a kasar Beljium yayi kakausan lafazi ga Kur'ani mai girma

  • Lambar Labari†: 667023
  • Taska : ABNA
Brief

Dan siyasar mai tsatsauran ra'ayi ya bayyana a gaban majalisar kasar dauke da Kur'ani a hannun sa inda ya bayyana cewar dukkan wani sharri ga tushan sa nan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna- Philip Dvyntr daya daga cikin masu tsananin kyama ga musulmi a kasar Beljium ya bayyana a gaban majalisar kasar inda yayi mumunar suka ga Kur'ani mai girma.

Yayin zaman majalisar kasar a kan abunda ya shafi lamuran masallatai da tsatsauran ra'ayi ,Philip Dvyntr daya daga cikin yan majalisar ya fito a gaban zauran taron yayin da yake kalubalantar mataimakin shugaban kasar John Ham, ya bayyana Kur'ani a matsayin tushen duk wani sharri, kuma ya kara da cewar; Kur'ani ya bada izinin kisa don hakan babu wani dalili da kwamnatin kasar zata taimaka ma masallatai ko kuma biyan limamai albashi.

A yayin jawabinsa John Ham ya nuna rashin jin dadin sa a kan furicin da Philip yayi a kan Kur'ani inda yace; wannan littafin dake hannunka wani abune mai tsarki kuma abun girmamawa ga wani sashe na yan kasar.

Mataimakin shugaban kasar ya gara da cewar duk da munsan da a kwai masu tsatsauran kishin addini a kasar kuma muna yaki da irin wannan  tunani,amma duk da haka abunda Philip ya fada a kan musulunci bai dace ba.ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni