Rasha Ta Ce Za Ta Mutunta Zabin Al'ummomin Gabaci Da Kudancin Kasar Ukraine

  • Lambar Labari†: 648828
  • Taska : http://hausa.irib.ir/
Brief

Gwamnatin Rasha ta sanar cewa za ta mutunta zaben da al'ummomin yankunan gabaci da kudancin kasar Ukaraine suka gudanar, wadanda shelanta ballewa daga kasar ta Ukraine bayan juyin mulkin da masu goyon bayan turawa suka yi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Inter-Fax ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar rasha ta fitar da bayani a safiyar yau Litinin da ke cewa, gwamnatin kasar za ta mutunta duk abin da al'ummomin yankunan Luhansk da Donetsk suka zaba, tare da kiran mahukuntan kasar ta Ukraine da su ajiye duk wani roman baka da kasashen yammacin turai suke yi musu, su koma su sasanta da al'ummominsu nag abaci da kudancin kasar, maimakon mayar da su saniyar ware da kaddamar da yaki a kansu.

 

Tun a cikin watan Fabrairun farkon wannan shekara ne dai masu tsatsauran ra'ayi a kasar ta Ukraine da ke samun goyon bayan Amurka da sauran kasashen yammacin turai suka yi wa gwamnatin Victor Yanukuvic juyin mulki wanda daya ne daga cikin 'yan kabilar Rashawan Ukrane, lamarin da ya jaza bore a yankunan kudanci da gabacin kasar, wanda kuma mazauna wadannan yankuna Rashawa ne, inda daga karshe yankin Cremia ya gudanar da jin ra'ayin jama'a kan hadewa da kasar Rasha, wanda asalin yankin na Rasha ne ta bayar da shi kyauta ga Ukraine. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky